News
’Yan Bindiga Sun Yi Ajalin Mutum 7, Sun Jikkata 11 A Sabon Hari A Kaduna
Aƙalla mutum bakwai ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu 11 suka jikkata a wani sabon hari da ’yan bindiga suka kai ƙauyen Wake da ke gundumar Agunu, a Ƙaramar Hukumar Kachia ta Jihar Kaduna.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 5:55 na safiyar Lahadi, lokacin da ’yan bindigar suka mamaye garin tare da yin ta’adi da harbe-harbe ba kakkautawa.
Farashin Kayan Abinci Ya Sauka A Kasuwanni, Amma Masu Dafa Abinci Sun Ki Rage Kuɗi —Rahoto
Bayan kashe mutum bakwai da jikkata wasu, maharan sun kuma yi garkuwa da wasu mazauna garin, duk da cewa adadin mutanen da aka sace bai bayyana ba a halin yanzu.
Waɗanda suka rasa rayukansu a harin sun haɗa da Elisha Paul, Japhet Bitrus, Obadiah Joshua, Luka Augustine, Ishaya Paul, Bawa Bulus da Ezekiel Augustine.
Daga cikin waɗanda suka jikkata kuwa akwai Gideon Pius, Zachariah Anthony, Moses Christopher, Uhu Sunday, Christopher Ishaya Sunday, Elisha Ishaku, Clement Godday da Janet Godday, waɗanda aka garzaya da su asibiti domin samun kulawa.
Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida cewa: “’Yan bindigar sun kashe mutum bakwai, sun jikkata da dama sannan suka yi garkuwa da wasu. Kullum cikin fargaba muke kwana.”
Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, ya ci tura, domin bai ɗaga kiran waya ba har zuwa lokacin da aka kammala wannan rahoto.
