Connect with us

News

Bishiya Ta Halaka Mutum Daya, Ta Jikkata Bakwai A Benue

Published

on

1 5

Wani mummunan hatsari ya faru a kauyen Ngimbo, Mbadam Mbatierev da ke karamar hukumar Gboko, Jihar Benue, inda wata bishiya ta fadi ta kashe mutum daya tare da jikkata wasu mutane bakwai.

Marigayin, wanda aka bayyana sunansa da Chiahemba Tarpav, ya rasu a ranar Juma’a, 19 ga Satumba, 2025. A halin yanzu dai wadanda suka jikkata suna karbar magani a wani asibiti na yankin.

An Gano Masana’antar Ƙera Makamai A  Filato

Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Benue, Rt. Hon. Hyacinth Aondona Dajoh, ya jajanta wa iyalan mamacin, inda ya biya kudin maganin wadanda suka jikkata tare da daukar nauyin shirya jana’izar marigayin.

 

 

 

Advertisement

DAILY POST

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending