Sports
Lamine Yamal Zai Shafe Mako 3 Yana Jinya

DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO
Matashin ɗan wasan gaban Barcelona da Sifaniya, Lamine Yamal zai shafe tsawon mako uku ya na jinyar raunin da ya samu a mararsa.
Yamal na daga cikin ‘yan wasan da tawagar Sifaniya ta kira domin buga wasannin neman gurbin buga gasar Kofin Duniya.
Mutane Da Dama Sun Mutu, Motoci Sun Kone Yayin Da Tankar Mai Ta Kama Da Wuta A Babbar Hanya
Yamal ya shafe kwanaki yana jinya kafin ya dawo filin wasa a wasan da Barcelona ta doke Real Sociedad da ci 2-1 a gasar Laliga, sannan kuma ya buga wasan da Barcelona ta yi rashin nasara a hannun PSG a gasar Zakarun Turai.
Sakamakon haka Yamal ba zai buga wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da ƙasar Sifaniya za ta kara da Georgia da Bulgaria a wannan watan in ji Barcelona a ranar Juma’a.
Ana sa ran ɗan wasan mai shekaru 18 da haihuwa zai yi jinyar makonni biyu zuwa uku, kocin Spain Luis de la Fuente ya ce tun da farko a ranar Juma’a cewa ba shi da wata matsala da kocin Barcelona Hansi Flick bayan sukar da ya yi kan yadda tawagar ƙasar ke tafiyar da matashin.