News
Wata Ɗaliba Ta Kamu Da Tabin Hankali Bayan Kallon Fim Ɗin Ban Tsoro A Makaranta
Wasu iyaye a China sun kai karar makarantar da ‘yar su ke yi bayan an gano tana fama da cutar tabin hankali wacce masana lafiya suka bayyana a turance da suna “acute and transient psychotic disorder”. Ana zargin cutar ta samo asali ne daga kallon fim ɗin ban tsoro da ɗalibar ta kalla a aji, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka ruwaito.
Rahotanni sun bayyana cewa wannan lamari ya faru shekaru biyu da suka wuce, amma sai a makon da ya gabata ne kotu ta kammala shari’ar.
Jirgin Ƙasa Ya Faɗi Kwanaki 4 Kacal Bayan An Shafe Watanni Ana Gyare-gyare A Najeriya
TRIBUNE ta rawaito cewa a watan Oktoba 2023, yayin da malaminsu ya ɗauki hutu na wuccin-gali, wasu ɗalibai a wani aji na makarantar da ke Hangzhou, lardin Guanxi, sun kalli wani fim a cikin aji.
Ko da yake ba a bayyana sunan fim ɗin ba, amma iyayen ɗaya daga cikin ɗaliban sun ce fim ɗin na ban tsoro ne kuma ya yi mummunan tasiri a ƙwaƙwalwar ‘yarsu.
An ce matsalar ta fara ne da yamma bayan kallon fim ɗin, lokacin da ɗalibar ta fara nuna alamun rashin lafiya, ciki har da rashin iya magana da juyewar kai.
Sakamakon wannan, iyayenta suka kai ta asibiti, inda likitoci suka gano cewa ta kamu da tabin hankali.
Daga nan ne iyayen ɗalibar suka shigar da makarantar kara a kotu, suna neman diyya ta dalar Amurka $42,000. Sun yi zargin cewa kallon fim ɗin ban tsoro ne ya janyo wa ‘yarsu matsalar tabin hankali, kuma makarantar ta kasa cika hakkinta na kula da tarbiyya da tsaron ɗalibai yadda ya kamata.
