News
Cutar Kwalara Ta Yi Ajalin Mutum 244 A Cikin Watanni 9 A Najeriya
Kungiyar Kiwon Lafiya ta Duniya WHO ta bayyana cewa cutar Amai da Gudawa wanda aka fi sani da Kwalara ta yi ajalin mutum 244 a tsakanin Janairu zuwa Satumba a Najeriya.
Hukumar ta ce a tsakanin watanni tara Najeriya ta samu mutum 10,353 da take zargin sun kamu da cutar.
Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba United
A tsakanin kwanaki 28 mutum 615 sun kara kamuwa da cutar sannan cutar ta yi ajalin mutum 10 a kasan.
“Zuwa yanzu mutum 10,353 ne ake zargin sun kamu da cutar inda cutar ta yi ajalin mutum 244 daga cikin mutum 100,000 sannan a kwanaki 28 din da suka gabata mutum 515 sun kamu sannanutim 10 sun mutu.
Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa NCDC ta ce daga ranar 27 ga Janairu zuwa 2 ga Fabrairu 2025 an samu mutum 886 da ake zargin sun kamu sannan cutar ta yi ajalin mutum 14.
Bisa ga rahotan da Hukumar ta gabata ya nuna cewa cutar ta bullo a jihohi 22 a Najeriya.
Kwararrun jami’an lafiya sun ce cutar na yawan bullowar ne saboda rashin tsaftace muhalli, amfani da ruwa mai tsafta da yawan samun ambaliyar ruwan dake ake fama da shi a Najeriya.
