Connect with us

News

Yadda ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari Ofishin Kwastam A Kebbi

Published

on

Nigerian Customs Officer

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari wani ƙaramin ofishin hukumar kwastam a jihar Kebbi tare da kashe wani jami’i guda ɗaya a ƙaramar hukumar Bagudo.

Hukumar talabijin ta ƙasa (NTA) ta rawaito cewa wasu gungun ‘yan ta’adda ne suka kai wa ginin wurin hari tare da harbin kan mai uwa-da-wabi kan jami’an da ke bakin aiki.

Advertisement

Dambarwar Tantance Ramat a Shugabancin NERC: Barau Yana Kyashin Samar Da Wuta Don Farfado Da Kamfanoni Kano — Barista S S Umar

Sadiq Muhammad, mataimakin sufurtanda ne, shi ne wanda ‘yan ta’addan suka kashe.

Mazauna yankin sun ce harin ya jefa su cikin firgici wanda ya sanya da yawansu tserewa cikin daji. Tuni aka aika da jami’an tsaro domin dawo da kwanciyar hankali a yankin.

Advertisement

An gudanar da jana’izarsa a fadar Abdullahi Fodio da ke Birnin Kebbi, kuma gwamnan jihar, Nasir Idris, da wasu manyan jami’an gwamnatin jihar sun halarci jana’izar.

A yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin, mai magana da yawun rundunar kwastam a jihar Kebbi, Salisu Tajuddeen, ya bayyana cewa sun rasa jami’i ɗaya inda ya ce, suna cigaba da bincike domin kama waɗanda suke da hannu kan harin.

Advertisement

Harin kan ofishin kwastam ɗin na zuwa ne ƙasa da mako ɗaya bayan ‘yan bindiga sun kai hari garin Bagudo tare da sace mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Muhammad Sama’ila.

An kama ɗan majalisar ne a garinsu na Bagudo a ranar Juma’a jim kaɗan bayan kammala sallar Isha’i.

Advertisement

Sai dai ya shaƙi iskar ‘yanci bayan an biya kuɗin fansa.

Jihar Kebbi na ɗaya daga cikin jihohin Arewa masi yamma da ke fama da matsalar ‘yan bindiga wanda ke haifar da yawan satar mutane da kashe-kashe a yankin.

Advertisement

 

PREMIUM TIMES

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending