News
REMASAB Da SFC Sun Horas da Masu Tattara Shara Kan Muhanmancin Tsaftar Muhalli A Kano
Hukumar Kula da Shara da Tsaftar Muhalli ta Kano (REMASAB) tare da kamfanin Sahcon Fumigation and Cleaning Services (SFC) sun gudanar da horo ga masu aikin tattara shara domin inganta tsarin tarawa da zubar da shara yadda ya kamata.
Daraktan REMASAB, Dr. Muhammad Khalil, ya ce gwamnati na ƙara ƙoƙari wajen inganta kula da shara ta hanyar horarwa, ƙarfafa dokoki da tsaurara bin ka’idojin biyan kuɗi. Ya bayyana cewa gwamnati da kamfanonin masu zaman kansu sun amince su haɗa kai wajen tabbatar da dokokin kula da shara a jihar.
“Kula da shara ba aikin gwamnati kaɗai ba ne; kamfanoni masu zaman kansu suna da muhimmiyar rawa a sassa daban-daban,” in ji shi.
Dr. Khalil ya ce rashin biyan kuɗi shi ne babban ƙalubale, amma sabuwar yarjejeniya za ta tilasta biyan kuɗi. Duk da an sanya kwandon shara a wurare kamar State Road, Race Course da Airport Road, har yanzu mutane da yawa ba sa bin ka’idoji.
Daraktan SFC, Dr. Sani Usaini, ya ce ya zama dole a bi ingantattun hanyoyin tattara shara, kula da lafiyar ma’aikata da kuma sake amfani da wasu kayan da ake jefawa.
“Yanzu babu shara da ba ta amfani. Komai za a iya mayar da shi arziki,” in ji shi.
Shugaban ƙungiyar masu kula da shara ta Kano, Dr. Bala Muhammad, ya roƙi gwamnati da ta ƙara tsaurara matakan tilasta biyan kuɗi, yana mai cewa rashin biyan kuɗi ya yi tasiri ga ayyukan kamfanoni masu zaman kansu. Ya bayyana cewa a wasu unguwanni, daga gidaje 100 kawai 15 zuwa 20 ke biyan kuɗi.
Ya yi maraba da kafa kotunan tafi-da-gidanka, yana mai cewa hakan zai tilasta bin doka.
> “Da kotunan tafi-da-gidanka, ba za a sake yin sakaci ba,” in ji shi.
