News
Jami’an Tsaron Ghana Sun Kama Ƴan Najeriya Kusan 50, Bisa Zargin Damfara Ta Yanar Gizo
Wani sumame da haɗakar jami’an tsaron Ghana suka gudanar kan ɓatagarin da ke damfara ta internet a birnin Accra fadar gwamnatin ƙasar ya kai ga kame ƴan Najeriyar da yawansu ya tasamma 50.
Ministan yaɗa labarai na ƙasar Ghana Sam George ya bayyana cewa an gudanar da samamen ne a cikin dare bayan da su ka shammaci masu aikata damfarar ta intanet, in da kuma jami’ansu su ka yi nasarar kame mutane 48 dukkaninsu ƴan Najeriya da ke shiga ƙasar don gudanar da ayyukan damfarar jama’a.
Yan Bindiga Sun Tare Hanya Sun Kwashe Mutane Da Dama A Zamfara
Ministan labaran na Ghana Sam George ya ce ƴan Najeriyar 48 sun ƙunshi maza 46 da kuma mata guda 2, waɗanda ke bijiro da salo na aikata laifukan damfarar jama’a galibi ga mazauna ƙasashen waje.
Wani saƙo da George ya wallafa a shafinsa na X na cewa wasu daga cikin laifukan da ƴan Najeriyar ke aikatawa ta Intanet akwai soyayyar ƙarya ta inda suke yaudarar ɗimbin mutane da sunan sun faɗa soyayya da su har ta kai ga sun karɓi maƙuden kuɗaɗe a hannunsu.
Haka zalika ministan labaran na Ghana ya ce akwai kuma waɗanda ke yin ƙaryar kasuwanci da neman masu zuba jari inda suke guduwa da kuɗin jama’a.
Cikin laifukan ƴan Najeriyar ta kafar intanet akwai kuma batun sayar da zinare shima dai na ƙarya.
A cewar minista George, yayin sumamen jami’an tsaron ƙasar sun kame na’urar laptop guda 54 da kuma wayoyin hannu 39 waɗanda da su ne ɓatagarin ke aikin damfarar da su.
