News
Yan Bindiga Sun Tare Hanya Sun Kwashe Mutane Da Dama A Zamfara
’Yan bindiga sun tare ’yan kasuwa daga ƙauyen Adafka da ke kan hanyar zuwa kasuwar Gurusu sun kashe mutum ɗaya tare da yin garkuwa da mutane 20 a yammacin Alhamis.
Karamar hukumar Bukuyum ta Jihar Zamfara ta sake fuskantar wani hari na ’yan bindiga suka kai hari a unguwar Adafka.
Fadar Shugaban Kasa ta karyata jita-jitar tsige Gbajabiamila
Wani mazaunin ƙauyen Adafka mai suna Malam Aminu Shehu ya ce ’yan bindigar sun far wa ‘yan kasuwar ne a hanyar su ta zuwa Gurusu yayin da wasu ke kan hanyarsu ta zuwa Gusau babban birnin jihar.
“ ’Yan bindiga sun tare hanya sun kashe mutum ɗaya tare da yin garkuwa da mutane da ba a tantance adadinsu ba amma aƙalla waɗanda aka sace sun haura 20, har yanzu muna tattara jerin sunayen waɗanda abin ya shafa.” In ji Shehu.
Da aka tambaye shi kan ƙoƙarin da hukumomin tsaro suka yi na ceto waɗanda aka yi garkuwa da su, Shehu ya ce jami’an tsaro sun taimake su domin ɗaukar gawar kuma suna shirye-shiryen binne shi.
“Eh, jami’an tsaro sun taimake mu ne kawai don mu ɗauki gawarwakin domin binne su.
An yi duk ƙoƙarin jin ta bakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar amma abin ya citura.
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
-
News1 day ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News15 hours ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
