Connect with us

News

Fadar Shugaban Kasa ta karyata jita-jitar tsige Gbajabiamila

Published

on

Femi Gbajabiamila
Spread the love

Fadar Shugaban Ƙasar Najeriya ta musanta jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sauya Shugaban Ma’aikatansa, Femi Gbajabiamila.

A wata sanarwa da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Tsare-tsare, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Alhamis, ya ce rahoton ba shi da tushe balle makama.

Jami’an Yan Sanda Sun Kama Mutane 5 Da Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane A Kano

Sanarwar ta ce an samu labarin ne a shafukan sada zumunta, inda ake ikirarin cewa an maye gurbin Gbajabiamila da Babban Sakatare na Musamman ga Shugaban Ƙasa, Hakeem Muri-Okunola.

Fadar Shugaban Ƙasa ta jaddada cewa duka biyun na ci gaba da gudanar da ayyukansu kamar yadda aka ɗora musu, kuma babu wani sauyi da aka yi.

Advertisement

“Shugaban Ma’aikata yana nan a kan muƙaminsa, haka kuma Babban Sakatare na Musamman yana nan a aikinsa. Babu wanda ya maye gurbin wani,” in ji sanarwar.

Fadar Shugaban Ƙasar ta bayyana rahoton a matsayin ƙirƙira da nufin tayar da ruɗani a cikin gwamnati, tare da yin kira ga kafafen yaɗa labarai da su riƙa tantance bayanai kafin wallafa su.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *