News
Shugaban Amuruka Donald Trump Ya Ce Sun Kawo Hare Hare Ga ‘Yan Ta’adda A Arewacin Najeriya
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce rundunar sojojinsa ta kai hare-hare kan wasu ‘yan ta’adda na ISIS a Arewacin Najeriya, a daren ranar Alhamis.
Trump ya bayyana haka ne a shafinsa na sada zumunta, Truth Social, inda ya ce da umarninsa ne hare-haren suka auku. Shugaban ya ce an kai hare-haren ne kan waɗanda ke kashe Kiristoci a Najeriya.
Jami’an Tsaron Ghana Sun Kama Ƴan Najeriya Kusan 50, Bisa Zargin Damfara Ta Yanar Gizo
“A daren yau, bisa umarnina a matsayin Babban Kwamanda, Amurka ta kai hare-hare masu ƙarfi da kisa kan ‘yan ta’addar ISIS a Arewa maso Yammacin Najeriya, waɗanda ke kai hare-hare da kashe fararen hula, musamman Kiristoci,” in ji Trump.
Ya ce tun a baya ya gargaɗi ‘yan ta’addar, inda ya nuna cewa za a hukunta su idan sun ci gaba da kai hare-hare kan Kiristoci.
Trump ya yaba wa rundunar Amurka kan yadda ta aiwatar da hare-haren, yana mai cewa:
Rahoton ya nuna cewa har zuwa yanzu ba a sami martani daga gwamnatin Najeriya ko sojojin ƙasar ba kan ikirarin da Trump ya yi.
-
News1 day ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News7 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
