Connect with us

News

Harin Amurka A Sokoto: Mazauna Garin Jabo Sun Tsira Daga Fashewar Bama-bamai

Published

on

FB IMG 1766709661430
Spread the love

Mazauna  garin Jabo da ke jihar Sokoto sun tsira daga fashewar bama-bamai da aka samu a garin ranar Alhamis, bayan da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa rundunar sojojin Amurka ta kai harin kan wasu ‘yan ta’adda na ISIS a Najeriya bisa umarninsa.

Mazauna garin sun ce babu wanda ya ji rauni a harin, yayin da suka nufi wuraren da fashewar ta auku domin ganin yanda abun ya faru.

Shugaban Amuruka Donald Trump Ya Ce Sun Kawo Hare Hare Ga ‘Yan Ta’adda A Arewacin Najeriya

Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa duk da hayaniyar da harin ya haifar, babu wanda ya ji rauni. Har yanzu ba a fitar da cikakkun bayanai kan yadda harin ya shafi sauran yankuna ba.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social ranar Alhamis, Donald Trump ya ce:

Advertisement

“A daren nan, bayan umarnin da na bayar a matsayina na Babban Kwamanda, Amurka ta kai gagarumin hari kan ‘yan ta’adda na ISIS a Arewa Maso Yammacin Najeriya, waɗanda suke kai hari da kashe mutane, musamman Kiristoci.”

Daga bisani, Cibiyar Bayar da Umarni ta Amurka a Afirka (AFRICOM) ta bayyana a shafin X cewa an kai harin ne a “Jihar Soboto inda aka kashe ‘yan ta’addan ISIS da dama”, wanda ake tsammanin ana nufin Jihar Sokoto.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *