News
CUTAR ƘODA: Akwai Sinadaran Ƙarfe A Cikin Ruwan Da Jama’ar Gashua Ke Sha —Bincike
Rahoton farko na binciken cutar ƙoda (ta CKD) da aka gudanar a Jihar Yobe ya nuna akwai sinadaran ƙarfe masu nauyi a cikin ruwan da jama’ar Gashua ke sha.
Farfesa Mahmoud Maina, Jagoran binciken kuma Darakta na Cibiyar Biomedical Research and Training Centre (BioRTC) a Jami’ar Jihar Yobe, Damaturu, ya bayyana hakan a hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN).
Bakin Haure Fiye Da 3,000 Suka Mutu A Yunkurin Shiga Turai A Shekarar 2025
Al’ummomin da ke bakin kogin Yobe, ciki har da Gashua da Jakusko, sun daɗe suna fama da matsalar gazawar ƙoda, wadda ta jawo mace-mace da nakasa.
Farfesan ya ce sinadaran ƙarfe irin su cadmium, dalma da arsenic na iya haddasa cutar ƙoda, kuma bai kamata su kusanci muhalli ba.
“Idan aka same su a kusa da muhalli, ba wai cutar ƙoda kaɗai suke haifarwa ba, har ma da cututtuka irin su ciwon daji da mantuwa,” in ji shi.
Rahoton ya kuma nuna cewa cutar suga da hawan jini na daga cikin manyan dalilan da ke tayar da CKD, inda aka gano cewa masunta sun fi kamuwa da cutar fiye da sauran jama’a.
BioRTC tare da tawagar masana kimiyya 50 daga Amurka, Birtaniya, Ghana da sauran ƙasashe, sun tattara fiye da samfurori 3,000 na mutane da muhalli – ciki har da fitsari, jini, abinci, ƙasa, da ruwan kogin da ruwan rijiyoyi.
Farfesa Maina, ya ce cikakken rahoto zai fito a watan Janairu 2026.
A kan binciken ciwon mantuwa da cibiyar ta ƙaddamar a Damaturu, ya ce an tattara bayanan rayuwa, jinin mutane 1,200 da aka ɗauka a matsayin masu haɗari, da kuma samfurin fatar jiki domin binciken kwayoyin halitta da gano alamomin cutar.
Dementia cuta ce da ke da alaƙa da mantuwa, wadda ke rikiɗewa zuwa ruɗani, ganin abubuwan da babu su, da kuma rasa ikon kula da kai.
