News
Abin Fashewa Ya Tashi A Babban Asibitin Bagudo Da Ke Kebbi
Rundunar ƴan sanda a jihar Kebbi ta tabbatar da afkuwar fashewar bam da sanyin safiyar Talata a babban asibitin Bagudo, da ke karamar hukumar Bagudo ta jihar.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Bashir Usman, ya fitar a Birnin Kebbi.
CUTAR ƘODA: Akwai Sinadaran Ƙarfe A Cikin Ruwan Da Jama’ar Gashua Ke Sha —Bincike
Usman ya ce: “Muna son tabbatar wa mazauna yankin cewa an shawo kan al’amuran tsaro gaba ɗaya bayan wata babbar ƙara ta fashewa da ta auku a babban asibitin Bagudo da sanyin safiyar Talata, 30 ga Disamba.
“Ƙungiyar tsaro ta haɗin gwiwa wadda ta ƙunshi ‘yan sanda, sojoji da ‘yan sa-kai ta kulle tare da tabbatar da tsaron yankin cikin gaggawa. Ƙwararrun jami’an EOD-CBRN suna wurin suna gudanar da cikakken bincike.
“Muna farin cikin sanar da cewa babu wanda ya rasa ransa. Duk da cewa wani gini a ɓangaren ma’aikata ya lalace, mazauna wajen sun riga sun fice lafiya.
“Kwamishinan ƴan sanda na jihar ya ƙara tura jami’an tsaro na musamman domin tabbatar da zaman lafiya da doka.”
