News
Tukunyar Gas Ce Ta Fashe Saboda Tsananin Zafi A Babban Asibitin Bagudo – Yansanda
Rundunar yansandan jihar Kebbi ta bayyana cewa fashewar da ta auku a Babban Asibitin Bagudo ba ta da alaƙa da bam ko wani hari.
A cewar rundunar, lamarin ya faru ne da safiyar ranar Talata, inda ya jefa al’umma cikin firgici, sai dai an tabbatar da cewa babu asarar rai.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar yansandan jihar, SP Bashir Usman, ya ce a cikin wata sanarwa, fashewar ta samo asali ne daga gobara da ta haifar da zafin gas na na’urorin AC da firinji, wanda hakan ya haddasa karar fashewa da aka ji.
Advertisements
