News
Jami’an ‘Yan Sanda Sun Kama Sama da Mutane 3,000, Sun Kwato Makamai Da Miyagun Ƙwayoyi A Kano A 2025
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta bayyana cewa ta samu gagarumar nasara wajen rage laifuka da tabbatar da zaman lafiya a fadin jihar a shekarar 2025, inda ta kama mutane 3,081 da ake zargi da aikata manyan laifuka daban-daban.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, PhD, ne ya bayyana hakan yayin gabatar da jawabin ƙarshen shekara ta 2025 a ranar 30 ga Disamba, 2025, a shelkwatar rundunar ‘yan sanda da ke Bompai, Kano.
Tukunyar Gas Ce Ta Fashe Saboda Tsananin Zafi A Babban Asibitin Bagudo – Yansanda
CP Bakori ya ce, bayan zaman sa kwamishinan ‘Yan sanda a ranar 17 ga Maris, 2025, rundunar ta tarar da kalubalen tsaro da suka hada da fadace-fadacen daba, fashi, satar wayoyi, barazanar ‘yan bindiga a kan iyakoki, da rikice-rikicen manoma da makiyaya a wasu kananan hukumomi.
A cewarsa, domin magance wadannan matsaloli, rundunar ta samar da tsare-tsare na zamani kamar community policing, amfani da bayanan sirri, horas da jami’ai, sintirin hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro, da kuma kaddamar da Operation Kukan Kura domin yakar daba da satar wayoyi.
Ya bayyana cewa daga Janairu zuwa Disamba 2025, an kama:
• Mutane 146 kan fashi da makami,
• 50 kan garkuwa da mutane,
• 112 kan dillancin miyagun ƙwayoyi,
• 85 kan satar motoci,
• da mutane 2,350 kan harkar daba.
•
Haka kuma, rundunar ta kubutar da mutane 14 da aka yi garkuwa da su.
CP Bakori ya kara da cewa an kwato makamai da kayayyaki masu yawa, ciki har da bindigogi na zamani da na gargajiya, alburusai, makamai masu kaifi, motoci, babura, wayoyin hannu, da kuma miyagun ƙwayoyi da suka hada da tabar wiwi, Tramadol, Codeine, Diazepam da sauran kwayoyi masu bugarwa.
Kwamishinan ya bayyana cewa wadannan nasarori sun haifar da raguwar laifuka a jihar, tare da samar da sabon yanayi na zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Dangane da shirin shekarar 2026, CP Bakori ya ce rundunar za ta kara fadada hulɗa da al’umma, inganta tattara bayanan sirri, kara sintiri, da kuma karfafa tsaro a kananan hukumomin da ke kan iyaka.
Ya kuma gwamnatin Jihar Kano, al’umma, sauran hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya, shugabannin addinai, kafafen yada labarai da jami’an ‘yan sanda bisa goyon baya da hadin kai, tare da addu’ar samun sabuwar shekara ta 2026 cikin lafiya da zaman lafiya
