News
Shekaru Hudu Da Rasuwar Fitaccen Malamin Hadisi, Sheikh Dr. Ahmad Ibrahim Bamba
A yau laraba, 7 ga watan Janairu, cikar shekaru huɗu kenan da rasuwar shahararren malamin addinin Musulunci kuma masani a fannin Hadisi, Sheikh Dr. Ahmad Ibrahim Bamba.
Marigayi Sheikh Dr. Ahmad Ibrahim Bamba ya rasu ne a ranar 7 ga Janairu, 2022, bayan gajeriyar rashin lafiya, inda ya kwashe kwana ɗaya a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano (AKTH) kafin Allah Ya karɓi rayuwarsa.
Sheikh Ahmad Bamba ya yi fice sosai a fagen koyar da ilimin Hadisi. A baya ya shafe shekaru yana karantarwa a Masallacin Jami’ar Bayero Kano (BUK), kafin daga bisani ya kafa nasa cibiyar ilimi mai suna Darul Hadis, wadda ta zama matattarar karatun Hadisi ga ɗalibai daga sassa daban-daban na Nijeriya da ma ƙasashen waje.
Marigayin ya kasance malami mai zurfin ilimi da kuma kwarewa ta musamman a fannin Hadisi, inda manyan malamai da ɗalibai da dama a faɗin duniya suka amfana da karatunsa da tarbiyyarsa. An san shi da tsantsar riko da Sunnah, tawali’u da jajircewa wajen yaɗa ilimin addinin Musulunci.
A bangaren iyali, marigayi Sheikh Dr. Ahmad Ibrahim Bamba ya rasu ya bar mata biyu, tare da ’ya’ya da jikoki. Daga cikin ’ya’yansa akwai waɗanda suka gaji ilimi da kyawawan siffofinsa, tare da ci gaba da tafiya a tafarkin da mahaifinsu ya shimfiɗa na hidimar addinin Allah.
Rasuwar malamin ta girgiza al’ummar Musulmi, inda manyan malamai, shugabannin addini da jama’a daga sassa daban-daban suka bayyana alhininsu tare da yi masa addu’o’i.
A madadin daukacin ma’aikatan jaridar INDA RANKA, muna addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya yalwata masa rahama, Ya kuma sanya Aljannar Firdausi ta zama makomarsa. Ameen.
