Connect with us

News

Jami’an ’Yan Sanda Sun Cafke Wani Shugaban Ƙungiyar Daba da Wasu Mutane Tara A Kano

Published

on

FB IMG 1759160530529

Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta ce ta cafke wani da ake zargi da zama shugaban wata ƙungiyar daba da ake nema ruwa a jallo, Sunusi Dawa Kamsusi, tare da wasu mutane tara, bisa zargin aikata laifuka daban-daban a wasu sassan birnin Kano.

Cafke waɗanda ake zargin ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da mazauna unguwannin Bachirawa, Kurna, Rijiyar Lemo, Zango, Kunture da maƙwabtansu suka gabatar, inda suka koka kan yawaitar fashi da makami, satar wayoyi, fasa shaguna da gidaje, safarar miyagun ƙwayoyi da lalata kayayyakin ’yan banga kamar yanda Kakakin Rundunar Ƴansandan jihar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a Ranar Jumma a.

Advertisement

Real Madrid Za Ta Sake Karawa Da Benfica A Wasan Cike Gurbi Na Gasar Zakarun Turai

Wata ƙungiyar matasa mai suna Hannu Da Yawa Youth Development Association (HADAYA) ta miƙa koken a rubuce ga rundunar ’yan sandan, tana roƙon ta ɗauki matakin gaggawa domin dawo da zaman lafiya a yankunan.

Advertisement

Bayan karɓar koken, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayar da umarnin tura jami’an sashen Anti-Daba domin gudanar da bincike. Rundunar ta ce binciken da aka yi tare da bayanan sirri ne ya kai ga cafke babban wanda ake zargi da wasu mambobin ƙungiyarsa.

A cewar ’yan sanda, an cafke Sunusi Dawa Kamsusi, mai shekara 26, mazaunin Bachirawa, inda aka same shi da wuƙaƙe uku da kuma wani abin da ake zargin tsafin kariya ne. An kuma kama wasu mutane tara da ake zargin mambobin ƙungiyar ne.

Advertisement

Rundunar ta ce yayin bincike, wanda ake zargin ya amsa aikata laifukan fashi da makami, satar wayoyi, fasa gidaje da shaguna, inda ta ƙara da cewa mutane kusan 30 sun riga sun shigar da ƙorafi a kansu.

’Yan sandan sun tabbatar da cewa za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike, tare da jaddada cewa ba za su lamunci duk wani nau’in aikata laifi ba a faɗin Jihar Kano.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending