News
Gwamnatin Tarayya Za Ta Yi Amfani Da Tsaffin Dakarun Sojin Wajen Yaƙi Da Ta’addanci
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce za ta fara amfani da tsaffin dakarun soji da suka yi ritaya domin taimakawa wajen yaƙi da ta’addanci a wasu sassan ƙasar da ke fama da matsalolin tsaro.
Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya ce matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na dawo da yankunan da ke ƙarƙashin ikon ƴan ta’adda, tare da tabbatar da dawowar cikakken tsaro da zaman lafiya.
Jami’an ’Yan Sanda Sun Cafke Wani Shugaban Ƙungiyar Daba da Wasu Mutane Tara A Kano
A cewarsa, tsaffin sojojin za su yi aiki ne tare da jami’an tsaro da ke bakin aiki, musamman a yankunan da ake fuskantar barazanar tsaro, domin ƙarfafa ayyukan tsaro da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Wata sanarwa da Ma’aikatar Tsaron Najeriya ta fitar a ranar Laraba ta ce matakin ya biyo bayan kafa wani kwamiti na musamman mai mambobi 18, wanda aka ɗora wa alhakin tsara hanyoyin dawo da yankunan da ke fama da matsalolin tsaro ƙarƙashin ikon gwamnati.
Sanarwar, wadda Enderline Chukwu ya sanya wa hannu a madadin Daraktan Yaɗa Labarai na ma’aikatar, ta ƙara da cewa an ƙaddamar da kwamitin ne tun a ranar Talata da ta gabata.
A yayin ƙaddamar da kwamitin a Abuja, Babban Sakataren Ma’aikatar Tsaro, Richard Pheelangwa, wanda ya wakilci ministan, ya ce za a zaɓi tsaffin sojojin bisa ƙwarewa da kishin ƙasa, yana mai cewa gogewarsu za ta taimaka wajen dakile dawowar ƴan ta’adda a wasu yankunan Najeriya.
