News
Kotu Ta Rufe NNPC Depo Na Hotoro Da Wasu Wurare
Hukumar Kula da Shara da Tsaftace Muhalli ta Jihar Kano (REMASAB), tare da haɗin gwiwar Kotun Tsaftace Muhalli ta jihar, ta rufe depot ɗin kamfanin NNPC da ke Hotoro, sakamakon rashin bin ƙa’idojin tsaftar muhalli.
Matakin ya biyo bayan wani aikin tilasta bin doka da hukumar ke gudanarwa domin tabbatar da tsaftace muhalli da kare lafiyar al’umma a faɗin jihar Kano.
Kotu Ta Rufe NNPC Depo Na Hotoro Da Wasu Wurare
Jami’in yaɗa labarai na REMASAB, Abubakar Ahmad, ya shaida wa Premier Radio cewa a yayin aikin, kotun ta gano wurare da dama da suka karya dokokin tsaftar muhalli, inda aka rufe wasu, yayin da aka ci tarar wasu.
Ya ce baya ga rufe depot ɗin NNPC da ke Hotoro, an kuma ci tarar wani gidan wanka da ke kan titin Hotoro bayan da aka same shi da laifin gurbata muhalli.
Abubakar Ahmad ya ƙara da cewa hukumar ta kama wasu da aikata laifukan lalata muhalli a unguwanni irin su Na’ibawa kusa da Royal City da kuma kan titin IBB, inda kotun ta ci tararsu tare da ba su wa’adin gyara domin bin ƙa’idojin tsafta.
A cewarsa, Shugaban REMASAB, Dr. Muhammad S. Khalil, ya yi kira ga al’ummar Kano da su bi dokokin tsaftar muhalli, yana mai jaddada cewa bin ƙa’idojin zai taimaka wajen kare lafiyar jama’a da samar da muhalli mai tsafta.
