News
Jami’an EFCC Sun Kama Tsohon Shugaban bankin Skye Bank, Tunde Ayeni Kan Zargin Badakalar Kuɗi
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC, ta kama tsohon shugaban bankin Skye Bank , Tunde Ayeni, bisa zargin aikata badakalar kuɗi mai yawa.
Jaridar TheCable ta rawaito cewa, rahotanni sun ce an cafke Ayeni ne a Abuja a ranar Alhamis, kuma yana hannun jami’an EFCC yayin da ake ci gaba da bincike a kansa.
Jami’an EFCC Sun Kama Tsohon Shugaban bankin Skye Bank, Tunde Ayeni Kan Zargin Badakalar Kuɗi
Hukumar na zargin cewa ya karkatar da kuɗaɗe da suka kai kimanin naira biliyan 36.5 da dala miliyan 30, waɗanda ake zargin an samo su daga bankin Polaris ta hannun wasu kamfanoni da ake alaƙanta da shi.
Ana sa ran ƙarin bayani zai fito daga hukumar yayin da bincike ke ci gaba.
Advertisements
