News
Rundunar ƴan sandan ta kori wasu jami’anta
Rundunar ƴan sandan Najeriya ta sanar da daukar mataki ladabtarwa kan harbe-harben da ya faru a ranar 26 ga watan Afrilun bana a garin Effurung na jihar Delta, wanda ya kai ga mutuwar wani Mr Mene Ogidi.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labaran rundunar ƴan sandan DCP Anthony Okon Placid ya fitar yau Laraba.
Hukumomin sun yanke hukuncin cewa jami’in ɗan sanda ASP Nuhu Usman ya aikata laifukan da suka saɓa da dokokin tsaro, da sauran sharuɗan amfani da makami.
A don haka, rundunar ƴan sanda ta kori ASP Nuhu Usman da sauran jami’an da aka kama da laifin aikata harbi ba bisa ƙa’ida ba.
Haka zalika, rundunar da za ta miƙa mutanen da suka aikata laifin zuwa ga hukumomin shari’a da ke da hurumin yanke musu hukunci.
-
News3 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News6 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News5 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
