News
Jami’an NDLEA Sun Cafke Mutane Uku Masu Buƙata Ta Musamman Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi
Jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa, NDLEA, sun cafke wasu mutane uku Masu buƙata ta musamman bisa zargin safarar miyagun ƙwayoyi a jihohin Anambra da Kwara.
Mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi, ya bayyana cewa jami’an NDLEA sun kama wani dattijo mai shekaru 60 mai suna Romanus Nwabara a dajin Akpaka da ke Onitsha bayan samun bayanan sirri kan harkokinsa.
Rikici Kan Rabon N8,000 Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Wani Matashi
A cewarsa, an samu Nwabara da gram 250 na tabar wiwi da aka rarraba cikin ƙananan buhuna domin sayarwa.
Haka zalika, jami’an hukumar sun kai samame a yankin Ogbunike na jihar Anambra inda suka kama wani mai Masu buƙata ta musamman mai suna Amos Kenneth mai shekaru 25 da haihuwa.
Rahoton ya ce an same shi da gram 160.3 na ƙwayoyin Tramadol 225mg da 100mg, ƙwayoyin Diazepam guda 80, gram 38.23 na Exol 5 da kuma gram 176.93 na tabar wiwi.
A jihar Kwara kuwa, jami’an NDLEA sun kama wani mai Masu buƙata ta musamman mai suna Usman Salisu bayan sun tare wata motar haya a hanyar Bode Saadu.
An ce jami’an sun gano kilogram 6.3 na tabar wiwi da aka ɓoye a cikin wata jakar makaranta mai launin ruwan kasa mallakinsa.
NDLEA ta kuma ce ta ci gaba da shirye-shiryen wayar da kan jama’a kan illar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi a makarantu, wuraren ibada da al’umma daban-daban a faɗin ƙasar.
