News
Tirela Ta Kife A Gadar Lado Da Ke Kano
Wata motar tirela da ke ɗauke da mashinan adaidaita sahu ta kife a gadar Ado Bayero, wadda aka fi sani da Gadar Lado, a Jihar Kano.
Rahotanni sun ce hatsarin ya afku ne bayan tirelar ta yi taho-mu-gama da wata mota kirar Honda da kuma wani babur din Adaidaita Sahu a gadar.
Lamarin ya haifar da cunkoson ababen hawa, yayin da jama’a da masu aikin ceto suka rika kai dauki domin kauce wa sake faruwar wani hatsari a yankin.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu rahoton asarar rai sakamakon hatsarin, sai dai ba a kai ga tabbatar da ko akwai wadanda suka samu raunuka ba.
Hukumomin da ke kula da zirga-zirga dai ba su fitar da cikakken bayani kan musabbabin aukuwar hatsarin ba zuwa yanzu.
-
News22 hours ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
