News
Rikicin ADC A Kano: Ibrahim Little Ya Musanta Zargin Ƙaƙabawa Jam’iyyar Shugabanni
Jigo a jam’iyyar ADC a Jihar Kano kuma mai neman takarar gwamna a zaɓen 2027, Alhaji Ibrahim Ali Aminu, wanda aka fi sani da Ibrahim Little, ya musanta zarge-zargen da ke cewa akwai wani yunƙuri na ƙaƙaba shugabanni ko ‘yan takara a cikin jam’iyyar.
A wata sanarwa da Adnan Mukhtar Tudun Wada, ANIPR ya fitar, Ibrahim Little ya ce dukkan matakan da ake ɗauka a jam’iyyar suna gudana ne bisa tanadin kundin tsarin mulkin ADC da kuma jagorancin shugabannin jam’iyyar na ƙasa.
Ya bayyana cewa rahotannin da ke yawo kan batun ba su da tushe, yana mai zargin wasu daga cikin mambobin jam’iyyar da ƙirƙirar bayanan da ka iya haddasa ruɗani da rarrabuwar kai a tsakanin magoya baya.
A cewarsa, wasu na amfani da kafafen yaɗa labarai da sada zumunta wajen ɓata sunan taron sasanci da aka gudanar domin samar da fahimtar juna da haɗin kai a cikin jam’iyyar kafin fara shirye-shiryen zaɓukan gaba.
Ibrahim Little ya ce babu wani mutum ko ƙungiya da ke da ikon tafiyar da jam’iyyar bisa ra’ayinta kaɗai, yana mai jaddada cewa dukkan matakai suna samun amincewar hukumomin ADC da suka dace.
Ya kuma yi kira ga mambobin jam’iyyar da su yi taka-tsantsan wajen karɓar bayanan da ba a tabbatar da sahihancinsu ba, tare da mayar da hankali kan ƙoƙarin bunƙasa jam’iyyar a Jihar Kano.
Jigon na ADC ya ƙara da cewa a shirye yake ya saurari duk wani ɓangare da ke da ƙorafi domin samar da maslaha da zaman lafiya a cikin jam’iyyar.
A ƙarshe, ya bayyana cewa ADC za ta ci gaba da bin tafarkin dimokuraɗiyya wajen zaɓen shugabanni da ‘yan takara, tare da tabbatar da cewa an bai wa kowa dama cikin adalci da gaskiya.
-
News7 days ago
Gwamnatin Kano Ta Umarci Masu Talla Da Masu Sana’ar Jari Bola Su Bar Karkashin Gadar Tal’udu
-
News3 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News3 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
