News
Zaɓen Gwamnan Bauchi 2027: ‘Yan Asalin Bauchi Mazauna Jihohin Arewa maso Yamma Sun Bayyana Goyon Bayansu Ga Usman Adamu Suphi
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Wasu ‘yan asalin Jihar Bauchi da ke zaune a jihohin shiyyar Arewa maso Yamma sun bayyana goyon bayansu ga Malam Usman Adamu Suphi domin ya zama gwamnan jihar a zaɓen shekarar 2027 ƙarƙashin jam’iyyar PDP.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwar manema labarai da Mai Daidaita Yaƙin Neman Zaɓen Suphi a shiyyar Arewa maso Yamma, Bello A. Bello (Nalardi), ya fitar a Kano bayan wani taro da masu ruwa da tsaki daga jihohi bakwai na shiyyar.
Yadda Aka Gano Gawar Wata Mata A Bandakin Coci
A cewar sanarwar, mahalarta taron sun bayyana cewa sun cimma matsayar mara wa Suphi baya ne saboda abin da suka bayyana a matsayin gogewarsa a harkokin gwamnati da wadanda ba na gwamnati ba. Da kuma irin gudunmawar da ya bayar wajen bunƙasa rayuwar al’ummar Bauchi tsawon shekaru.
Sanarwar ta bayyana Suphi a matsayin gogaggen akanta, ƙwararren mai tsara dabarun siyasa, jagoran wayar da kan jama’a, mai ayyukan jin ƙai da kuma mutum mai sadaukar da kai wajen yi wa al’umma hidima.
Ta kuma yi iƙirarin cewa ya taimaka wajen samar da ayyukan yi ga matasa sama da 200 a hukumomin tarayya da suka haɗa da FIRS, NCC da CBN, tare da ba da gudunmawa wajen ɗaukar sama da matasa 300 aiki a rundunar ‘yan sanda, sojoji, DSS, Kwastam da Hukumar Gidajen Gyaran Hali.
Bugu da ƙari, sanarwar ta ce Suphi ya tallafa wa matasa da mata da jarin kasuwanci na ɗaruruwan miliyoyin Naira, ya kuma ɗauki nauyin aurar da marayu da dama, tare da ba da motoci, babura da kuma tallafin zuwa aikin Hajji da Umara ga mutane da dama.
A cewar sanarwar, ɗaya daga cikin manyan ayyukan da yake gudanarwa shi ne gina cibiyar koyar da fasahar sadarwa da rubuta jarabawar CBT mai ɗaukar mutum 850 a Azare, wadda ake sa ran za ta faɗaɗa damar koyon fasaha da samar da aikin yi ga matasa.
Game da tarihin siyasarsa, sanarwar ta ce Suphi ya kwashe fiye da shekaru 20 yana fafutuka a siyasa, inda ya riƙe muƙamai daban-daban a jam’iyyun PDP, APC da NNPP, kafin ya koma PDP a shekarar 2025.
Ta ce a halin yanzu yana cikin Kwamitin Amintattu (BoT) na jam’iyyar PDP a Jihar Bauchi.
Sanarwar ta ƙara da cewa ‘yan asalin Bauchi mazauna jihohin Arewa maso Yamma sun shirya gudanar da irin wannan taron goyon baya a kowace jiha ta shiyyar domin ƙarfafa wa takarar Suphi gwiwa gabanin zaɓen 2027.
Haka kuma, ta yaba da yadda ake ci gaba da samun ƙarin masu rajistar zaɓe a Bauchi, inda ta buƙaci al’ummar jihar su ci gaba da yin rajista domin su samu damar kaɗa ƙuri’arsu a babban zaɓen shekarar 2027.
-
News7 days ago
Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Kai Ziyarar Ba Zata Asibitin Kwararru Na Best Choice Dake Kano
-
Uncategorized3 days ago
Samar Da Zaman Lafiya, Ayyukan Ci Gaba Sun Isa Shugaba Tinubu Ya Samu Wa’adi Na Biyu — Kwankwaso
-
News5 days ago
El-Rufa’i Ya Shigar Da Ƙarar Neman Diyyar Biliyan N10 Bisa Zargin ICPC Da Nesanta Shi Da Iyalansa
