Connect with us

News

Barcin Direban Tirela Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 15, Ya Jikkata Wasu 17 A Kwara

Published

on

Akalla mutane 15 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu 17 suka jikkata sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya afku a kusa da maƙabartar Musulmi da ke kan hanyar Ogbomoso–Oko Olowo, a kan babbar hanyar Ilorin zuwa Jebba, a Jihar Kwara.

Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) ta bayyana cewa hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:32 na safiyar Litinin, inda ya shafi wata tirela kirar DAF XF mai lambar rajista GWL 274 XC

Zaɓen Gwamnan Bauchi 2027: ‘Yan Asalin Bauchi Mazauna Jihohin Arewa maso Yamma Sun Bayyana Goyon Bayansu Ga Usman Adamu Suphi ‎

A cewar hukumar, mutane 48 ne, dukkansu maza, ke cikin motar lokacin da hatsarin ya faru. Daga cikinsu, mutane 15 sun mutu nan take, 17 sun samu raunuka daban-daban, yayin da sauran 16 suka tsira ba tare da sun ji rauni ba.

FRSC ta danganta musabbabin hatsarin da gajiyar direba, wanda ake zargin ya yi barci yayin tuƙi, lamarin da ya haddasa motar ta rasa hanya. Hukumar ta ce waɗanda suka jikkata sun samu raunuka da suka haɗa da karayar ƙashi, gocewar gaɓoɓi da kuma munanan buguwa.

Kwamandan FRSC na Jihar Kwara, Kabiru Kazeem, ya bayyana sunan direban motar da Nasiru Muhammed. Ya ce an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa Arewa Medical Centre da kuma Baki Hospital domin ci gaba da kula da lafiyarsu.

Advertisement

Ya ƙara da cewa an miƙa gawarwakin mamatan ga iyalansu tare da haɗin gwiwar Sarkin Hausawan Oko Olowo da ke Ƙaramar Hukumar Moro ta Jihar Kwara.

Kazalika, Kazeem ya ce jami’an FRSC na ofisoshin RS8.15 Oloru da RS8.1 Oko Olowo ne suka gudanar da aikin ceto, yana mai cewa ana ci gaba da bincike domin tabbatar da ko akwai wasu da kaya suka rufe bayan afkuwar hatsarin.

A ƙarshe, kwamandan ya ce hukumar za ta ƙara ƙaimi wajen wayar da kan direbobi da masu ababen hawa kan muhimmancin bin ƙa’idojin hanya. Ya kuma yi kira ga direbobi da su guji haɗa fasinjoji da kaya a mota guda, su huta yadda ya kamata kafin tafiya, sannan su guji yin tafiye-tafiye cikin dare domin rage yawan haɗurran da ake samu a kan tituna.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending