Connect with us

News

Shugaba Tinubu Ya Ba Da Umarnin Binciken Meta Da X Kan Amfani Da Labaran Najeriya

Published

on

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bai wa hukumar kare haƙƙin masu saye FCCPC umarnin fara bincikar manyan kamfanoni irinsu Meta da X, da kuma shafukan da ke ƙirƙirar hotuna da bidiyo da fasahar AI, kan zargin amfani ko kuma satar ayyukan kafofin yaɗa labaran ƙasar.

Wannan ya biyo bayan takardar ƙorafi ta haɗin gwiwa da Ƙungiyar ƴan jarida ta NPO da ƙungiyoyin NPAN, da NUJ da BON da GOCOP ke ƙarƙashinta suka aike wa gwamnatin tarayyar Najeriya.

Barcin Direban Tirela Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 15, Ya Jikkata Wasu 17 A Kwara

Umarnin gwamnatin ga hukumar FCCPC na cikin wata wasiƙa da Ministan yaɗa labarai da wayar da kai, Mohammed Idris ya rattabawa hannu.

A cewar sanawar, binciken zai mayar da hankali wajen yin duba game da ƙorafin da kafafen yaɗa labaran suka gabatar, kan tasirin irin waɗannan ayyuka a tsarin yaɗa labaran ƙasar.

Takardar ƙarar ta bayyana sunayen manyan kamfanoni irinsu Meta, da Alphabet da X wanda aka fi sani da Twitter, da wasu shafukan da ake amfani da AI waɗanda ke aiki a Najeriya, inda suke zarginsu da rashin mutunta dokoki, da kuma satar ayyukansu, ko ma sauya musu ma’ana.

Advertisement

Da yake martani game da umarnin, Shugaban FCCPC, Tunji Bello ya ce hukumar za ta gudanar da sahihin bincike a bayyane kuma mai ɗauke da hujjoji.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending