Connect with us

News

Yadda Aka Gano Gawar Wata Mata A Bandakin Coci

Published

on

An gano gawar wata mata mai suna Blessing Ayebe a cikin bandakin wata coci da ke unguwar Ikot Ansa a birnin Calabar, hedikwatar jihar Cross River, lamarin da ya jefa al’umma cikin jimami.

Rahotanni sun nuna cewa marigayiyar ta halarci ibada a cocin Presbyterian Church, Ikot Ansa Parish a ranar 28 ga watan Yuni, amma ba ta koma gida bayan an kammala taron ba, abin da ya sa iyalanta suka fara neman ta.

An Caka Wa Wani Mutum Wuƙa Har Lahira  Yayin Da Suke Gardama

Bayan kwana guda ana nemanta, an gano gawarta a cikin bandakin cocin da misalin ƙarfe 9:00 na dare a ranar 29 ga watan Yuni, kamar yadda majiyoyi daga iyalanta suka bayyana.

‘Yarta, Peace Minka Ayebe, ta kai rahoton lamarin ofishin ‘yan sanda na Federal Housing Police Station bayan ɗan uwanta, Saviour Ayebe, ya sanar da ita gano gawar.

Daga nan ne aka kai gawar zuwa ɗakin adana gawarwaki na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Calabar (UCTH), inda za a gudanar da binciken likitoci domin gano ainihin musabbabin mutuwarta.

Advertisement

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Cross River, ASP Eitokpah Sunday Akata, ya ce binciken farko da aka gudanar bai gano wata alamar tashin hankali ko raunuka a jikin marigayiyar ba.

Ya ƙara da cewa har yanzu ba a kama ko gano wanda ake zargi ba, domin babu wata shaida da ke nuna cewa an aikata laifi.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending