News
An Caka Wa Wani Mutum Wuƙa Har Lahira Yayin Da Suke Gardama
Wani mutum mai shekaru 36, Charles Ekuma Eze, ya rasa ransa bayan da ake zargin wani mutum ya caka masa wuƙa a yayin wata takaddama da ta ɓarke a Ƙaramar Hukumar Ikom ta Jihar Kuros Riba.
Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi a ƙauyen Etayip da ke garin Ikom, sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto ba a bayyana ainihin abin da ya haddasa takaddamar da ta rikide zuwa tashin hankali ba.
Yadda Farfesa Gwarzo Ya Zama Fitaccen Jagoran Raya Ilimi Da Bunƙasarsa A Nahiyar Afirka
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Kuros Riba, ASP Eitokpah Sunday Akata, ya ce ana zargin wani mutum mai suna Micheal Ndifon mai shekaru 42 da caka wa marigayin wuƙa a gefen haƙarƙarinsa na dama yayin da suke gardama.
Ya bayyana cewa shugaban rundunar tsaron al’umma (Task Force) na yankin, Ndifon Nkang, tare da shugaban matasa na al’ummar Asse-Asin, Felix Agbor, ne suka kai rahoton faruwar lamarin ga ofishin ’yan sanda na Ikom.
A cewarsa, an garzaya da marigayin zuwa Asibitin Holy Family da ke Ikom domin ba shi agajin gaggawa, kafin daga bisani a tura shi zuwa Asibitin Koyarwa na Jihar Ebonyi da ke Abakaliki, inda ya rasu yayin da yake karɓar magani.
Kakakin rundunar ya ce jami’an ’yan sanda sun kama wanda ake zargi da aikata laifin, tare da ƙwato wuƙar da ake zargin an yi amfani da ita wajen caka wa mamacin.
Ya ƙara da cewa an kai gawar mamacin ɗakin ajiye gawa domin gudanar da gwajin gano musabbabin mutuwarsa, yayin da aka ce za a miƙa binciken lamarin ga Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar (SCID) domin ci gaba da bincike da ɗaukar matakin doka.
-
News7 days ago
Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Kai Ziyarar Ba Zata Asibitin Kwararru Na Best Choice Dake Kano
-
Uncategorized2 days ago
Samar Da Zaman Lafiya, Ayyukan Ci Gaba Sun Isa Shugaba Tinubu Ya Samu Wa’adi Na Biyu — Kwankwaso
-
News5 days ago
El-Rufa’i Ya Shigar Da Ƙarar Neman Diyyar Biliyan N10 Bisa Zargin ICPC Da Nesanta Shi Da Iyalansa
