Connect with us

News

Gwamnonin Jihohi Huɗu Sun Yi Wa Fursunoni 257 Afuwa

Published

on

Aƙalla fursunoni 257 ne aka saki daga gidajen gyaran hali a jihohin Filato da Kogi da Taraba da Adamawa, bayan gwamnonin jihohin sun yi musu afuwa da sauran sassaucin hukunci a bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun ’yancin kai.

A Jihar Filato, Gwamna Caleb Mutfwang ya yi wa fursunoni 130 cikakkiyar afuwa, yayin da ya sauya hukuncin kisa na wasu fursunoni huɗu zuwa ɗaurin rai da rai.

Ruwan Famfo Na Daf Da Dawowa A Kano: Madalla Gwamna Abba 

A Jihar Kogi kuwa, Gwamna Usman Ododo ya yi wa 101 daga cikin fursunoni da waɗanda aka yanke wa hukunci afuwa ko sassaucin hukunci.

Gwamna Agbu Kefas na Jihar Taraba ya yi wa 24 daga cikin fursunonin da suka gyara halayensu afuwa, yayin da Gwamna Ahmadu Fintiri na Adamawa ya yi wa tara afuwa tare da sauya hukuncin kisa na wani fursuna zuwa ɗaurin rai da rai.

Jimillar fursunoni da waɗanda aka yanke wa hukunci 264 ne suka samu wani nau’i na afuwa ko sassaucin hukunci a jihohin huɗun, yayin da 257 daga cikinsu suka samu damar fita daga gidan gyaran hali.

Advertisement

Gwamnonin sun ce an ɗauki matakin ne bisa la’akari da halayen fursunonin, gyaran halin da suka samu, yanayin lafiyar su da yin nadama da kuma jinƙai.

 

 

AMINIYA

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending