Connect with us

Labarai

Majalisar Dattawa Ta Ba Wa Jihohi Huɗu Wa’adin 17 Ga Nuwamba Kan Ƙudirin Yansandan Jihohi

Published

on

9
Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Jagoran Sanatoci, Sanata Opeyemi Bamidele ya ce, sauran majalisun dokokin jihohi suna da har zuwa ranar Talata, 17 ga Nuwamba, 2026 na su miƙa rahotanninsu kan matsayarsu game da Ƙudirin kafa ‘Yan Sandan Jihohi gabanin komawar Majalisar Dokokin Ƙasa bakin aiki. Bamidele ya bayyana cewa, jihohi 32 sun riga sun amince da ƙudirin na State Police (Constitution Alteration) Bill, 2026.

Ya bayyana haja ne a wata sanarwa da aka fitar a ranar Lahadi a Abuja bayan karɓar kyautar karramawa ta jaridar The Sun ta Gwarzon Sanatan Shekara kan jagorancin majalisa da samar da dokoki. A cewarsa, tuni shirin kafa ‘yan sandan jihohi ya wuce muhawara zuwa tabbas musamman bisa la’akari da Sashe na 9(2) da Dokar Ƙasa ta 1999 da ya hukunta neman amincewar wani kaso na jihohi faɗin Nijeriya.

Matasa Uku Sun Mutu Yayin Ƙoƙarin Ciro Waya Daga Masai A Zariya

Sanatan ya ce, jihohi huɗu ya rage su bayar da rahoton ba’asinsu kan al’amarin, yana mai cewa wajibi su miƙa a ranar 17 ga Nuwamba ko kafin lokacin, wato ranar da Majalisar Dokokin Ƙasa za ta koma aiki daga hutun da ta je. Ya bayyana cewa, gaɓa ta gaba bayan haka ita ce aike wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na ya amince da ita a dokance.

Wannan yunƙurin ya zo ne a daidai lokacin da ayyukan ɓarayin daji, garkuwa da mutane, rikicin ƙabilanci da sauran ayyukan ta’addanci da suke neman fin ƙarfin hukumomin tsaron da ake da su a Nijeriya.

Bamidele ya ce adadin jihohin da suka amince ya wuce abin da kundin tsarin mulki ya tanada na kashi biyu bisa uku na majalisun dokokin jihohi 36, wanda ya yi daidai da jihohi 24. Shugaban masu rinjayen ya bayyana cewa tsarin gyaran kundin tsarin mulkin ya ƙunshi matakai uku da suka haɗa da amincewar Majalisar Dokoki ta Ƙasa, amincewar aƙalla kashi biyu bisa uku na majalisun dokokin jihohi, da kuma sanya hannun shugaban ƙasa.

Advertisement

 

 

PUNCH

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending