Uncategorized
Cutar Mashaƙo Ta Yi Ajalin Mutane Sama Da 1,100 A Najeriya

Ƙungiyar agaji ta ƙasa da ƙasa ta Médecins Sans Frontières (MSF) ta yi gargaɗin cewa ƙarancin maganin cutar Mashaƙo na ƙara jefa rayukan marasa lafiya cikin haɗari a Arewacin Najeriya.
Ƙungiyar, wadda aka fi sani da Doctors Without Borders, ta bayyana cewa ƙarancin maganin Diphtheria Antitoxin (DAT) ya kai wani mataki mai tayar da hankali, wanda ke tilasta wa ma’aikatan lafiya rage adadin maganin da suke bai wa marasa lafiya.
Jami’an Ƴansanda Sun Kama Mutane Takwas Bayan Rikicin Siyasar Da Ya Barke A Bichi
MSF ta ce sama da mutum 28,000 ne suka kamu da cutar a Najeriya a shekarar 2026, yayin da fiye da mutum 1,100 suka mutu sakamakon cutar.
A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Juma’a, ƙungiyar ta bayyana cewa maganin DAT na da muhimmiyar rawa wajen dakile gubar da ƙwayar cutar ke samarwa a jikin mutum, wadda ke haddasa matsalolin lafiya masu tsanani da ka iya zama barazana ga rayuwa.
Ta ce ƙarancin maganin na ƙara ƙalubalantar ƙoƙarin ma’aikatan lafiya na kula da masu fama da cutar, musamman a yankunan da cutar ta fi kamari.
Gargaɗin na MSF na zuwa ne yayin da bayanan da aka danganta da Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Ƙasa (NPHCDA) da cibiyoyin sa ido kan cututtuka suka nuna cewa cutar na ci gaba da yaɗuwa a Najeriya, musamman tsakanin yaran da ba su samu cikakkiyar rigakafinta ba.
Saboda haka, ƙungiyar ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi, masu bayar da tallafi da abokan hulɗar ƙasa da ƙasa da su gaggauta samar da isassun magungunan DAT da alluran rigakafi domin shawo kan matsalar.
Haka kuma, MSF ta buƙaci hukumomin da abin ya shafa da su hanzarta kammala matakan shigo da magungunan cikin ƙasar, tare da inganta tsarin rarraba su zuwa yankunan da cutar ta fi yaɗuwa.
Ƙungiyar ta jaddada cewa samar da magungunan cikin gaggawa da ƙarfafa rigakafi su ne muhimman matakai wajen rage mace-macen da cutar ke haddasawa.
-
Labarai6 days ago
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Yi Wa Masu Digirin Ƙasashen Waje Jarrabawa
-
Labarai2 days ago
Jami’an Tsaro A Pakistan Sun Kama ’Yan Najeriya 20 Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi
-
Labarai1 day ago
Hare-haren Ta’addanci Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 835 A Najeriya Cikin Wata Guda – Rahoto
