Connect with us

News

NLC ta soma gudanar da gagarumar zanga-zanga a Abuja

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAH

 

 

Kungiyar kwadago ta Najeriya, NLC ta fara wata gagarumar zanga-zanga yau Laraba a Abuja, domin nuna goyon bayanta ga sauran kungiyoyin ma’aikata da ke yajin aiki saboda jami’o’in gwamnati da ke ci gaba da kasancewa a rufe.

Tun da farko Babban Sakataren kungiyar ta NLC, Emmanuel Ugboaja ya bayyana a wata sanarwa da Bello Ismail ya sanya wa hannu a madadinsa cewa za su yi gangamin a babban birnin tarayyar.

Zaɓen 2023 zai kasance ingantaccen darasi a ƙasashen Afrika -Buhari.

Malaman jami’o’in gwamnati Najeriyar da sauran wasu kungiyoyin ma’aikata a bangaren ilimi na yajin aiki sama da wata biyar saboda gazawar gwamati ta cika alkawarin yarjejeniyar da ta yi da kungiyoyin.

Advertisement

Tun a jiya Talata ne kungiyoyin kwadago suka fara zanga-zangar a fadin jihohin kasar domin matsa wa gwamnati lamba kan ta biya bukatun kungiyoyin ma’aikatan na bangaren ilimi, domin a bude jami’o’in.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending