Connect with us

News

Kwastam ta ƙwace ƙwayar tramadol da ta kai darajar naira biliyan ɗaya a Legas

Published

on

Kwastam

DAGA MUJAHID DANLAMI GARBA 

 

 

 

 

Dakarun hukumar kwastam a Najeriya ta kama wata kwantena maƙare da haramtacciyar ƙwayar a-ji-garau ta tramadol a tashar Apapa ta Jihar Legas mai darajar fiye da naira biliyan ɗaya.

Advertisement

 

Wani rahoto da hukumar ta wallafa a shafinta na sada zumunta ranar Juma’a ya ce masu kwantenar sun bayyana kayan ciki a matsayin tukunyoyi na girki, kuma suka biya biliyan 1.3 a matsayin kuɗin kayan.

Isra’ila ta kashe Falasɗinawa 10 a hare-hare kan Zirin Gaza

Sai dai da jami’an kwastam suka buɗe kayan sai suka tarar da katan-katan na tramadol ƙunshe a cikin tukunyoyin 273.

 

“Kowane katan na ƙwayar na ƙunshe da kwali 50, kowane kwali na ƙunshe da fakiti 10, kowane fakiti na da ƙwaya 10,” a cewar Kwantirolan Kwastam na Apapa Malanta Yusuf.

Advertisement

 

Kwastam ta ce ta ƙwace kayan kuma ta miƙa su ga hukumar NDLEA mai yaƙi da ta’ammali da miyagiun ƙwayoyi a Najeriya.

 

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending