News
Ganduje ya nada makusancin shekarau a matsayin kwamishina
Daga Yasir sani Abdullahi
Gwamnan kano Dr Abdullahi Umar ganduje ya aikawa da majalisar dokokin jahar kano da sabbin sunayen kwamishinoni takwas domin tantance su
Abun mamaki shine yadda akaga sunan Wani makusancin tsohon gwamnan jahar kano kuma senatan kano malan Ibrahim shekaru hon garba Yusuf abubakar
Garba na daga cikin ahalin gidan Sardaunan Kano da yayi bara’a komawarsa jam’iyyar NNPP ta tsohon gwamna Kwankwaso.
A kwanakin baya ne dai ahalin Shura na gidan siyasar Malam Ibrahim Shekarau suka bayyana goyon bayansu ga Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje tare da barranta kansu ga bin tsarin tsohon jagoran su Malam Ibrahim Shekarau.
Wadan da aka aika da sunayen nasu sun hada da
1,Ibrahim Dan azumi gwarzo
2/ garba Yusuf abubakar
.Adamu Abdu Fanda
4 .Yau Abdullahi Yan Shana
5 .Sale kausari
6 .Yusuf Jibrin Ruruwai
7 .Abdulhamid Abdullahi Liman
8 .Lamin Sani Zawiyya
A yanzu dai haka an bukaci Wanda aka Mika da sunayensu gaban majalisa da suje a tantance su ranar litinin dinnan Mai zuwa dazata kama 22/august/2022
source of siyasarmu
