News
Mai saida kaji ya zama zababben shugaban kasa
Daga Yasir sani Abdullahi
Williom ruto ya zama zabebben shugaban kasar Kenya Wanda Hakan yake ta jawo ce,ce kuce ga Al,ummar kasar da wasu kasashe rayuwar sa irin ta talakawa ce
BBC Hausa ta rawaito Williom Wanda shine shugaban kasar Kenya yanzu ya kasance dan talakawane sosai Wanda har ya fara faraimare bai da takalmin sawa har Sai,da ya shekara goma Sha biyar Sannan ya mallaka
Sannan ya yi sana’ar sayar da kaji da gyaɗa a bakin titi a ƙauyensu da yake yankin Rift Valley.
Don haka ba abin mamaki ba ne don ya nuna kansa a matsayin gwarzon talakawa, a lokacin da ya tsaya takarar shugaban ƙasa na 9 ga watan Agusta.
Mr Ruto ya tsaya takarar ne a ƙarƙashin gamayyar jam’iyyar Kenya Kwanza, wacce ta yi alkawarin haɓaka tattalin arzikin Kenya.
Rashin aikin yi a tsakanin matasa masu shekara 18 zuwa 34 ya yi kusan kashi 40 cikin 100, kuma tattalin arzikin ba ya samar da isassun ayyukan da za su taimaka wa matasa 800,000 da ke neman aiki a kowace shekara.
Hakan ne ya sa ya ƙirƙiri wani take “Hustler nation” wato “Ƙasar matasa masu fafutuka”, yana mai alaƙanta ta da matasan da ke ƙoƙarin samun na rufin asiri.
Mr Ruto ya yi alkawarin ɗaukar matakan gyaran tattalin arziki daga ƙasa zuwa sama, yana mai cewa hakan zai amfani talakawa waɗanda su ne suka fi shiga tsanani na hauhawar farashin da ke addabar duniya sakamakon ɓarkewar annobar cutar korona da kuma yaƙin Ukraine.
Wannan ne karo na farko da Ruto mai shekara 55 ya tsaya takarar shugaban ƙasa, kuma ya bai wa masu sukarsa mamakin nasarar da ya yi – duk da cewa dai mafi yawan mambobin hukumar zaɓen sun yi watsi da sakamakon suna mai cewa cike yake da maguɗi.
Sai dai shugaban hukumar zaɓen Wafula Chebukati, ya ce zaɓen sahihi ne, inda ya ayyana Mr Ruto a matsayin wanda ya yi nasara da kashi 50.5 na yawan ƙuri’un.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
