Kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki ta G7 ta takaita farashin man fetur da suke saya daga Rasha, a wani yunkuri na rage wa kasar kudin da take amfani da su a yakin Ukraine
Ministocin kudi na kungiyar sun ce takunkumin da za a sanya kan danyen man fetur din, zai haifar da saukar farashin makamashi a fadin duniya.
Nijeriya komai ya lalace a mulkin APC – Makarfi
Ministocin sun kuma ce ”za mu ci gaba da nuna goyon baya ga kasar Ukraine matukar ba a daina wannan yaki ba”
Kasashen G7 din – wadanda su ne ke juya kasuwanci da harkokin kudade na duniya – sun hadar da Burtaniya, da Amurka, da Canada, da Faransa, da Jamus, da Italiya da kuma Japan
