Business
Farashin kayan abinci ya sauko cikin watanni biyar a jere’
DAGA KHADIJA ABDULLAH MUHMD
Hukumar abinci da ayyukan gona ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce farashin kayan abinci ya sauka cikin watanni biyar a jere.
Hukumar ta ce bude hanyoyin fitar da kayan abinci kamar alkama da man girki da daga Ukraine ya taimaka wajen saukar farashin kayan abincin.
Kazalika bunkasa noman alkama a arewacin Amurka ma ya taimaka wajen saukar farashin kayan abincin.
Nijeriya komai ya lalace a mulkin APC – Makarfi
Haka kuma an samu karuwar fitar da kayayyaki daga Australia da kuma Brazil.
Sai dai wasu kwararru sun ce har yanzu akwai damuwa a kan fitar da kayan abincin saboda yanayin da ake ciki na damuna da kuma tsananin zafin da ake fuskanta a wasu kasashen turai da Pakistan ka iya shafar yanayin.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
