Connect with us

Business

Har ila yau, darajar Naira ta ragu a kasuwar canji

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADINNI

 

 

 

 

A ranar Juma’ar da ta gabata ne dai darajar Naira ta yi kasa a gwiwa idan aka kwatanta da dala a tagar masu zuba jari da masu fitar da kayayyaki, inda aka yi musanya akan N431.50.

Advertisement

Alkaluman ya nuna an samu karin kashi 0.35 cikin dari, idan aka kwatanta da N430 da aka yi musayar dala a ranar Alhamis.

Nijeriya komai ya lalace a mulkin APC – Makarfi

Farashin budaddiyar farashin ya rufe kan N429.10 zuwa dala a ranar Juma’a.

Canjin N444 zuwa Dala shi ne mafi girman farashin da aka samu a cinikin yau kafin ya daidaita kan N431.50.

Ana siyar da Naira a kan N418 zuwa dala a kasuwar ranar.

An yi cinikin dala miliyan 93.54 a tagar masu saka hannun jari da masu fitar da kayayyaki a hukumance ranar Juma’a.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending