News
Kazalika, Rugujewar Gini Ta Kashe Yara 3 A Jigawa
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar wasu yara uku a wani gini da ya rufta a karamar hukumar Dutse.
Solacebase ta bayar da rahoton rugujewar wani gini da ya yi sanadiyar mutuwar wata matar aure a karamar hukumar Gwaram ta jihar Jigawa, bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya, a daren Lahadi.
Najeriya na fitar da kayayyaki da ya kai N7.4trn-(NBS)
Jami’in hulda da jama’a na rundunar (PPRO), DSP Lawan Shiisu, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa a Dutse ranar Alhamis.
Shiisu ya ce lamarin ya faru ne da safiyar Laraba a unguwar Yakasai da ke kauyen Jigawa Tsada sakamakon ruwan sama da aka samu a yankin.
“A yau da misalin karfe 9:50 na safe ne aka samu labari daga kauyen Jigawar Tsada da ke karamar hukumar Dutse, cewa a wannan rana gini daya ya ruguje a yankin sakamakon ruwan sama da aka kwashe tsawon awa daya ana yi a daren jiya.
“Yara uku wato; Daya Farida Idi, 6, Mariya Idi, 3 da Bilkisu Yahya, daya da rabi, dukkansu Yakasai a Jigawar an ruwaito sun mutu nan take kafin a ceto su,” in ji Shiisu.
Ya bayyana cewa da samun rahoton ‘yan sanda sun zarce wurin da lamarin ya faru, inda suka kwashe wadanda lamarin ya rutsa da su aka garzaya da su zuwa babban asibitin Dutse, inda wani Likitan da ke bakin aiki ya ba da shaida cewa sun mutu.
PPRO ta kara da cewa tuni aka sako gawar mamacin ga iyalansu domin yi musu jana’iza.
