Connect with us

News

Farashin Abinci Ya Ragu A Duniya In Ji Majalisar Dinkin Duniya

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

 

 

 

 

Advertisement

 

Majalisar Dinkin Duniya ta ce farashin abinci a duniya ya ragu a cikin watanni shida a jere, bayan ya yi tsadar da rikicin Ukraine ya haddasa.

Hukumar da ke kula da abinci da aikin gona a Majalisar ta ce faduwar farashin man girki ita ce ta taimaka wajen raguwar farashin kayayyakin abincin.

Abin da Ministan Sufurin Najeriya ya ce kan dawo da jigilar jirgi tsakanin Abuja-Kadunap

Bincike ya nuna cewa farashin madara da nama da kuma sukari duk sun fadi idan aka kwatanta da baya.

To amma farashin alkalama ya tashi saboda rashin nomanta sosai da ba a yi ba a wasu yankuna, da kuma damuwar da ake da ita cewa ba lallai ne a sake sabunta yarjejeniyar da aka cimma ta barin fitar da kayan abinci daga Ukraine ba a karshen watan nan na Oktoba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending