Connect with us

News

Dan Takarar Gwamnan Jihar Kano A Jam’iyyar PRP Yakasai Ya Nada Suhaib Gwagwarwa A Matsayin Kakakin Yakin Neman Zaben sa.

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

 

 

 

 

Advertisement

 

Dan takarar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar PRP Salihu Tanko Yakasai (Dawisu) ya nada Suhaib Auwal Gwagwarwa a matsayin kakakin yakin neman zabensa.

Nadin na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun dan takarar gwamna na jam’iyyar PRP Salihu Tanko Yakasai kuma aka rabawa manema labarai a Kano .

Shaaban Sharada Ya Nada Abbas Yushau A Matsayin Kakakin Majalisar Yakin Neman Zaben Gwamna

A cewar sanarwar, Mista Suhaib dan jarida ne mai cikakken iko da gogewa a TV, Rediyo, aikin jarida na yanar gizo da kuma Social Media.

Malam Suhaib ya fara aikin jarida ne a gidan rediyon Freedom Kano, kuma ya kai matsayin mai bayar da rahoto da kuma kodinetan kafafen yada labarai na zamani. Ya yi aiki a Liberty TV, Kaduna (Labarai da Editan Bidiyo).

Advertisement

Mista Suhaib ya kuma yi aiki da wasu kafafen yada labarai na kan layi a Kano, wadanda suka hada da Solacebase da Daily News 24 .

Har zuwa wannan nadin, Mista Suhaib yana aiki da Gaskia TV (Satellite TV da ke Ghana) a matsayin mataimakin shugaban ofishin Kano, da Premier Radio a matsayin mai ba da shawara kan kafofin watsa labarai na Digital Media.

Sabon Kakakin Yakin Neman Zaben Gwamna na PRP ya samu Masters a Mass Communication a Jami’ar Igbinedion Okada da ke Jihar Edo, kuma ya halarci kwasa-kwasai da karatuttuka da dama a ciki da wajen Najeriya.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending