News
Yan Bindiga Sun Sace Mutane Hudu A Birnin Gwari
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Wasu ‘yan bindiga a safiyar yau, 24 ga Oktoba, 2022 (da misalin karfe 7:00 na safe) sun yi garkuwa da mutane hudu daga Layin Mahuta, Tabanni a karamar hukumar Birnin-Gwari.
An yi garkuwa da su ne a lokacin da suke dawowa daga kauyukan da ke makwabtaka da su a kan iyakar jihar Kaduna da Katsina.
(1) SANI LIMAN ( masallacin Imam Juma’at, Layin Mahuta, Tabanni)
(2) ALIYU SIDI
(3) ISAH ABDULLAHI
(4)UMAR MOHAMMED
A ‘yan kwanakin nan ne ‘yan ta’addan suka kai wa mutane hari a kauyen Tashar Bawa da ke jihar Katsina a karshen kan iyaka da jihar Kaduna.
Advertisements
