Connect with us

Business

Elon Musk zai zama sabon shugaban Twitter

Published

on

Ilon Musk

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

 

 

 

 

Advertisement

 

 

Ilon Musk ya bayyana cewa shi ne zai zama sabon shugaban kamfanin sada zumunta na Tuwita wanda ya saya kan zunzurutun kuɗi dala biliyan arba’in da huɗu.

Ɗaya daga cikin matakan farko da ya ɗauka bayan kammala cinikin kamfanin, shi ne korar shugaban kamfanin wato Parag Agrawal.

Sai dai masu sharhi na ganin da wuya zai mayar da hankali domin kula da kamfanin na Tuwita sakamakon irin ayyukan da suka sha masa kai a kamfanoninsa na Tesla da Space – X.

Haka kuma Mista Musk ya rushe daraktocin kamfanin duk da cewa ya ce matakin na wucin gadi ne.

Advertisement

Ana ganin zai kawo tsare-tsare masu yawa kan yadda ake gudanar da kamfanin ciki har da sauyi kan shafukan da aka tantance da shuɗin maki.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending