Connect with us

News

An ci tarar gidan talabijin na Arise saboda yaɗa ‘labarin ƙarya’

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Hukumar kula da kafafen yaɗa labaru na Najeriya NBC ta ci tarar kafar yaɗa labaru ta Arise saboda zargin ta da yaɗa labarin ƙarya.

 

Advertisement

A ƙarshen makon da ya gabata ne Arise TV ya yi wani labari da ke cewa hukumar zaɓe na binciken ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, bisa dogaro da wani labarin da aka rinƙa yaɗawa a shafukan intanet.

Sauya Fasalin Naira: Buni Ya Bukaci Karin Bankuna A Yobe 

NBC ta ce abin da kafar Arise ta yi, “gagarumin karan-tsaye ne ga dokar yaɗa labaru ta ƙasa sashe na 5.1.3, da rashin iya aiki, da kuma rashin tunani a wannan lokaci da ake yaƙin neman zaɓe.”

Advertisement

 

Saboda haka sanarwar wadda ta samu sa hannun shugaban hukumar, Balarabe Shehu Illela, ta buƙaci Arise TV ya biya tarar naira miliyan biyu a cikin wa’adin mako biyu.

Advertisement

 

A ranar Lahadi ne dai kafar Talabijin ɗin na Arise ya nemi afuwar ɗan takarar shugabancin Najeriya na jam’iyyar A.P.C, bayan da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta fitar da wani bayani kan cewar labarin da ake yaɗawa da ke cewa tana bincike kan Bola Ahmed Tinibu ba gaskiya ba ne.

Advertisement

 

Hukumar ta NBC ta kuma buƙaci kakafen yaɗa labaru da su rinƙa tantance duk wani labari da suka samu gabanin wallafa shi, musamman ma wanda aka samu a shafukan sada zumunta.

Advertisement

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending