News
Netherlands ta nemi gafara akan bautar da bakaken fata
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Firaministan Netherlands Mark Rutte ya nemi gafarar daukacin mutanen da kasar ta bautar ko kuma yiwa mulkin mallaka na shekaru 250, matakin da ya bayyana a matsayin cin zarafin Bil Adama.
Wannan neman gafarar tana zuwa ne shekaru 150 bayan kawo karshen mulkin mallakar da kasashen Turai suka yiwa yankunan dake kasashen ketare da suka hada da Suriname da kuma tsibirai irin su Curacao da Aruba dake Yankin Caribbean da kuma Indonesia.
FRSC ta baza jami’anta a sassa Najeriya domin bikin kirsimati da sabuwar shekara
Rutte wanda ke jawabi a Hague, yace a matsayinsa na jagoran gwamnatin Netherlands, yana neman gafara akan matakan da gwamnatin kasar ta dauka a wadancan lokuta.
Firaministan yace ‘mu da muke rayuwa ayau ya zama mana wajibi muyi Allah wadai da murya mai karfi saboda irin illar da tayi wajen cin zarafin Bil Adama’.
Gwamnatin Netherlands tayi nata mulkin mallakar ne a karni na 16 da kuma 17 wajen kwashe akalla bakaken fata 600,000 daga Afirka a matsayin bayi zuwa Yankin Kudancin Amurka da Caribbean.
A wadancan lokuta Netherlands ta mallaki yankunan da suka hada da Suriname da Tsibirin Curacao da kasashen Afirka ta Kudu da kuma Indonesia.
Sakamakon guguwar ‘Black Lives Matter’ da ta kada daga Amurka, anyi ta matsawa biranen Amsterdam da Rotterdam da Hague da kuma Utretch lamba da suma su nemi gafara game da rawar da suka taka wajen bautar da jama’a.
A baya Firaminista Rutte yaki amincewa da bukatar inda yace daukar matakin zai haifar da tankiya, amma kuma daga bisani ya bada kai bori ya hau.
Fri
