News
Sabon Kwamishinan Yan Sandan Kano Ya Kama Aiki.
Sabon kwamishinan rundunar yan sandan jihar Kano CP Muhammad Yakubu ya kama aiki, bayan dauke tsohon kwamishina, Mamman Dauda, zuwa jihar Plateau domin gudanar da zaben 2023.
Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a Talatar nan.
Gwamnoni uku sun kai ƙarar Emefiele da Malami kan raina kotu
Sanarwar tace rundunar ta tura, CP Ita Uko-Udom, a matsayin wanda zai kula da shiyar Kano ta tsakiya a zaben, sai kuma DCP Adamu Isa Ngoji da DCP Abdulkadir El-Jamil za su kula da shiyar kudancin Kano yayin da DCP Abaniwomda S.Olufemi zai kula da shiyyar Kano ta Arewa don kula da harkokin zaben.
Kiyawa yace sabon kwamishinan ya tabbatar wa al’ummar Kano cewa za a yi zabe mai tsafta.
