Connect with us

Politics

DA DUMI-DUMI || Jam’iyun Siyasa hudu a jihar Kano sun marawa sha’aban sharada baya

Published

on

A daidai lokacin da babban zaɓe ke kara ƙaratowa wanda ya rage ƙasa da kwanaki 21 a gudanar da zaɓen gwamnoni a faɗin ƙasar nan wasu ‘yan takarar gwamna a jihar Kano sun hamɓarar da tafiyarsu tare da marawa ɗan takarar Jam’iyyar ADP Sha’aban Sharaɗa baya.

‘Yan takarar sun janye takarar tasu ne da nufin marawa Sha’aban baya a zaɓen gwamnoni mai zuwa a ƙoƙarin su na ganin sun ceto jihar Kano, daga halin da ta tsinci kanta a cewar su, kamar yadda majiyar jaridar indaranka ta ruwaito

Advertisement

Amurka ta gargaɗi China kan bai wa Rasha tallafi a yakin Ukraine

Hakan dai na cikin wata sanarwa da kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen ɗan takarar ADP ya fitar Abbas Yusha’u, ya ce ‘yan takarar sun fito daga jam’iyyu daban-daban da su ka haɗa da Furera Ahmad ta jam’iyar BT, Aishatu Mahmud daga jam’iyar NRM, Ibrahim Muhammad na APGA sai kuma mataimakin ɗan takarar gwamna na jam’iyar APP.

Da yake jabi yayin karbar ‘yan takarar ɗan takarar gwamna kuma ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙwaryar birnin Kano, Hon. Ibrahim Sha’aban Sharaɗa ya bayyana jin daɗinsa tare da yin maraba da ƙudirinsu na ɗinkewa waje daya don haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen ceto jihar Kano.

Advertisement

Sharada ya kuma yiwa al’ummar jihar Kano albishir da cewa a sati mai zuwa za a ƙaddamar da wani bigeren adana bayanai na yanar gizo da za ayi amfani da shi wajen baiwa ‘yan jihar Kano kimanin Dubu 50 tallafi.

Da su ke jawabi kan maƙasudin barin jam’iyyun na su tare da marawa ɗan takarar jam’iyar ADP bayan ‘yan takarar sunce kyakkyawan ƙudirinsa na tallafawa marayu da matasa da kyawawan manufofinsa ne suka sanya su yanke shawarar mara masa baya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending