Politics
NNPP Ta Baiyana Bukatar Atiku Na Yin Sabuwar Maja A Matsayin Shan Magani Bayan Mutuwa
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Manyan jam’iyyun hamaiyya na kasar sun fara mayar da martani kan kiran da ‘dan takarar shugaban kasa a zaben da ya gabata karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya yi, inda ya baiyana cewar kamata ya yi jam’iyyun Hamaiyyar su hade wuri daya domin karbe mulki daga hannun jam’iyyar APC.
Jaridar Inda Ranka ta ruwaito cewa Atiku Abubakar ya baiyana bukatar yin sabuwar Majar ne a yayin da ya karbi bakuncin shugabannin majalisar bada shawarwari a tsakanin jam’iyyu ta kasa a Abuja ranar Talata.
A martanin da jam’iyyar Labour ta yi ta hannun mukaddashin sakataren yada labaranta Obiora Ifoh, Ya baiyana yunkurin hadewar wuri daya a matsayin wani abu da ya d ace, wanda kuma ya kamata ayi nazari kansa.
Haka zalika itama jam’iyyar NNPP ta hannun sakataren yada labaranta na kasa Yakubu Shendam, ya baiyana kiran da Atikun ya yi a matsayin abun jan hankali sannan kuma magani ne bayan mutuwa.
Ya kara da cewar za’a yadda da bukatar Atikun ne kadai idan har zai goyi bayan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso domin ya karbo mulki daga hannun jam’iyyar APC a shekarar 2027.
A wani labarin kuma Kungiyoyin Kwadago Sun Sanar Da Janye Yajin Aikinsu
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
